EU ta bukaci gaggauta ficewar dakarun Eritrea daga yankin Tigray
Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci sojojin Eritrea da su gaggauta ficewa daga 'yankin da ake samun tashin hankali a Tigray na kasar Habasha kamar yadda ta yi alkawari.
Wallafawa ranar:
Babban jami’in diflomasiyar kasashen Turai Josep Borrell ya ce ba a samun cigaban kirki a yankin Tigray, yayin da ake cigaba da gwabza fada da kuma fama da matsalolin ayyukan jinkai.
Jami’in ya shaidawa ministocin harkokin wajen Turai cewar Eritrea ta amince da rawar da ta taka a Tigray, yayin da ta yi alkawarin janye dakarunta daga cikin Habasha.
An dai kwashe watanni gwamnatin Habasha da takwararta ta Eritrea na musanta cewar dakarun Eritrea na cikin kasar a yankin na Tigray da ya yi fama da rikici.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu