Isa ga babban shafi
Habasha - G7

Kasashen G7 sun bukaci gaggauta janye dakarun Eritrea daga Tigray

Kungiyar G7 ta kasashe da suka fi karfin tattalin arziki, ta bukaci gaggauta janye sojojin Eritrea daga yankin Tigray mai fama da rikici dake arewacin kasar Habasha.

Sojojin kasar Eritrea a kauyen Adigrat dake yankin Tigray na kasar Habasha.
Sojojin kasar Eritrea a kauyen Adigrat dake yankin Tigray na kasar Habasha. © Baz Ratner/Reuters
Talla

Kiran na kasashen G7 na zuwa ne bayan da kungiyar ICG mai bibiyar tashe-tashen hankula tayi gargadin cewa yanayi a yankin na Tigray na dada yin muni, sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen TPLF da dakarun Habasha da kuma na Eritrea a gefe guda.

A makon jiya Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya  sanar da cewa dakarun na Eritrea za su fice daga yankin, kwanaki uku bayan da ya amince suna cikinsa.

A baya bayan nan kungiyoyi kare hakkin dan adam gami da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun yi ta kokawa kan zarge-zargen aikata laifukan yaki a yankin na Tigray da suka hada da kisan gilla, azabtarwa dakuma fyade.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.