Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Tigray ta dau alhakin harin roka a Eritrea

Shugaban yankin Tigray na Habasha ya yi ikirarin kaddamar da hare-haren makaman roka kan filin jiragen sama na babban birnin Eriteria mai makwabtaka da kasar, matakin da ya kara haifar da fargabar kazancewar tashin hankali a yankin na Tigray.

Dimbim yan Ethiopia da suka taru a wani dandali don bayar da gudumuwar jini ga mayakan kasar
Dimbim yan Ethiopia da suka taru a wani dandali don bayar da gudumuwar jini ga mayakan kasar AFP
Talla

Jami’an Diflomasiya sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, an kai hare-haren makaman roka a birnin Asmara na Eriteria a karshen mako, inda makaman suka dira a kusa da filin jiragen saman birnin.

Dakarun Habasha dai na amfani da wannan filin jirgin saman kamar yadda tsagerun Tigary suka bayyana cewa, inda suke ganin ya halatta su kai wa filin jirgin farmaki.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ce, ya bada umarnin kaddamar da aikin soji a yankin na Tigray a daidai lokacin da tankiyarsa da jam’iyyar tsagerun da ke mulkin yankin ta tsananta.

Jam’iyyar ta TPLF ta zargi gwamnatin Abiy da samun tallafin soji daga Eriteria, ikirrain da gwamnatin ta musanta.

Yanzu haka dai, wannan rikici ya tilasta wa Habashawa sama da dubu 25 tserewa daga muhallansu domin neman mafaka a Sudan , adadin da zai ci gaba da karuwa a cewar hukumomin Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.