Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Gwamnatin Habasha ta cafke sojojinta 17 saboda taimakawa 'yan tawaye

Gwamnatin Habasha ta cafke sojoji 17 bisa zargin su da cin amanar kasa, bayan ta zarge su da hada baki da hukumomin arewacin yankin Tigray domin yi wa kasar zagon-kasa.

Wani mayakin tawayen yankin Tigray na kasar Habasha
Wani mayakin tawayen yankin Tigray na kasar Habasha REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Firaminiatan Habasha, Abiy Ahmed ya aike da dakaru tare da jiragen sama na yaki zuwa jihar Tigray a makon jiya bayan an kwashe tsawon wata guda yana takun saka da jam’iyyarsa wadda ya ke zargi da kokarin jefa kasar cikin rikici.

Abiy wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a bara, ya zargi kungiyar TPLF ta mutanen Tigray da wuce gona da iyaka, ganin yadda suka kai wa sojoji hari a sansanoninsu guda biyu. Sai dai jam’iyyarsa ta musanta batun.

Yanzu haka kafar yada labarai ta gwamnati FBC ta rawaito daga majiyar ‘yan sanda cewa, an kama jami’an soji su 17 saboda zargin su da taimaka wa tsagerun TPLF wajen kaddamar da farmaki kan sansanin sojojin.

Bayanai na cewa, sojojin 17 sun kaste hanyar sadarwa tsakanin sansanonin da babbar cibiyar sojin arewacin Tigray, matakin da ake gani a matsayin cin amanar kasa.

Daga cikin wadanda ake zargi har da shugaban sashen sadarwa na rundunar sojin yankin wanda kuma aka cafke shi a daidai lokacin da yake kan aika wa tsagerun akwatina 11 dauke da abubuwan fashewa.

Tuni dubban mutane suka tsere daga yankin na Tigray, inda suka nemi mafaka a yammacin Sudan

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.