Eritrea ta amince da taimakawa sojojin Habasha a yankin Tigray
Eritrea ta amince da kasancewar ta a yankin Tigray na kasar Habasha wajen shiga cikin rikicin da sojojin gwamnati suka fafata da ‘yan awaren yankin dake neman ballewa.
Wallafawa ranar:
Eritea ta tabbatar da hakan ne karon farko ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya jiya Juma’a, inda ta amince ta fara janye dakarunta daga yankin na Tigray dake Habasha, bayan taimakawa dakarun Abiy Ahmad.
Amincewar cikin wata wasika zuwa ga mambobin kwamitin 15 - wanda kuma ma'aikatar yada labarai ta Eritrea ta sanya a intanet - ya zo ne kwana daya bayan da shugaban agaji na Majalisar Dinkin Duniya Mark Lowcock ya ce, ba su ga wata hujja da ke nuna cewa sojojin Eritrea sun janye daga yankin ba.
Eritiriya ta sha musanta batun a baya
Sojojin Eritiriya sun taimakawa sojojin gwamnatin tarayyar Habasha wajen yakar tsohuwar jam’iyya mai mulki ta Tigray a rikicin da ya fara a watan Nuwamba. Kodayake, Eritrea ta sha musanta cewa dakarunta suna yankin mai tsaunuka.
Firayinministan Habasha Abiy Ahmed a watan da ya gabata ya amince da kasancewar Eritriya kuma Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun bukaci sojojin Eritriya su fice daga Tigray.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu