Isa ga babban shafi
Habasha-Eritrea

Amnesty ta zargi sojojin Eritrea da kashe daruruwan fararen hula a Tigray

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International tace dakarun Etritrea sun yiwa daruruwan fararen hula kisan gilla a Tigray mai fama da rikicin ‘yan tawayen TPLF, yankin da suka yi iyaka da shi daga bangaren arewacin Habasha.

Wasu daga cikin dubban mutanen da suka tsere daga yankin Tigray a kasar Habasha, sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin 'yan tawayen TPLF da dakarun gwamnati.
Wasu daga cikin dubban mutanen da suka tsere daga yankin Tigray a kasar Habasha, sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin 'yan tawayen TPLF da dakarun gwamnati. AP - Nariman El-Mofty
Talla

Cikin rahoton da ta fitar a ranar Juma’a 26 ga watan Fabarairu, Amnesty ta bayyana kisan gillar a matsayin ta’asa babba da ka iya zama laifin yaki.

Amnesty tace ta tattara hujjojinta ne bayan ganawa da wasu daga cikin fararen hular da suka tsira daga kisan gillar dakarun kasar ta Eritrea su 41, sai kuma hotunan da ta samu daga tauraron dan adam, wadanda suka nuna yankunan da aka tafka mummunar ta’asar.

Sai dai ministan yada labaran Eritrea Yemane Gebremeskel yayi watsi da rahoton, wanda ya bayyana a matsayin yunkuri na shafawa kasarsa kashin kaji.

Tun cikin watan Nuwamba ake gwabza fada tsakanin sojojin Habasha da ‘yan tawayen TPLF a yankin Tigray, bayan da Fira Minista Abiy Ahmad ya bada umarnin afka musu, bayan da suka  kaddamar da farmaki kan sansanonin sojojin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.