Isa ga babban shafi
Habasha-Tigray

HRW ta zargi Sojin Habasha da kai farmaki kan farar hula a yankin Tigray

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi sojojin gwamnatin Habasha da kai harin sama kan birane lokacin da aka samu tashin hankali a yankin Tigray a watan Nuwambar bara, matakin da ya sabawa dokokin duniya.

Wasu Sojin Habasha a yankin Tigray.
Wasu Sojin Habasha a yankin Tigray. Tiksa Negeri/Reuters
Talla

Kungiyar ta ce daga wuraren da sojojin suka kai hari da makaman atilare har da gidajen jama’a da makarantu da asibitoci da kuma kasuwanni a biranen da ke yankin, abinda ya yi sanadiyar kashe mutane 83 cikin su harda mata da yara da kuma jikkata mutane sama da 300.

Kungiyar da ke kare hakkokin 'yan yankin ta ce mutanen da aka kashe sun zarce dubu 50, yayin da gwamnati ta yi watsi da adadin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.