Isa ga babban shafi
Habasha

Habasha za ta bada lada mai tsoka ga wanda ya gano maboyar 'yan tawayen Tigray

Gwamnatin Habasha ta yi alkawarin bada kyautar dalar Amurka dubu 260 ga duk wanda ya taimaka mata da bayanai kan maboyar shugabannin ‘yan tawayen TPLF na yankin Tigray.

Wasu daga cikin sojojin kasar Habasha a garin Sanja, dake lardin Amhara da yayi iyaka da yankin Tigray.
Wasu daga cikin sojojin kasar Habasha a garin Sanja, dake lardin Amhara da yayi iyaka da yankin Tigray. REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo
Talla

Shelar bada ladan da gwamnatin Habashar ta yi a wannan Juma’a na zuwa ne bayan da majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa jami’an agaji sun gaza isa ga miliyoyin yara a yankin Tigray na kasar Habasha, inda ake fafata kazamin fada tsakanin dakarun kasar da ‘yan tawayen TPLF.

Cikin rahoton da ta fitar majalisar dinkin duniyar ta ce akalla yara miliyan 2 da dubu 300 ne a yanzu haka suka gaza samun agajin gaggawa tun bayan barkewar rikici a yankin na Tigray, a farkon watan Nuwamba.

A ranar 12 ga watan Disambar nan kayayyakin agaji suka soma isa ga yankin na Tigray a karon farko, tun bayan da yaki ya barke tsakanin ‘yan tawayen yankin na TPLF da kuma dakarun gwamnati sama da wata daya da ya gabata.

Kwamitin bada agajin gaggawa na kasa da kasa Red Cross ya ce manyan motoci bakwai ne dauke abinci, magunguna da sauran kayayyakin bukata suka isa Makele babban birnin yankin na Tigray mai yawan mutane akalla dubu 500.

A karshen watan Nuwamba Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed ya umarci sojojin kasar da su kaddamar da farmakin karshe kan shugabannin yankin Tigray, yana mai cewa, wa’adin da aka ba su na mika wuya ya kawo karshe.

Abiy wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar bara ya bai wa kungiyar tsagerun na TPLF wa’adin sa’o’i 72 domin ajiye makamansu, sai dai shugabannin yankin na Tigray sun yi watsi da wa’adin, inda kuma dakarunsu suka ci gaba da gwabza fada da sojojin gwamnatin Habasha, abin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, baya ga sama da dubu 40 da suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.