Isa ga babban shafi
Tigray

Kayayyakin agaji sun isa yankin Tigray na Habasha

A karon farko kayayyakin agaji sun isa yankin Tigray dake kasar Habasha, tun bayan da yaki ya barke tsakanin ‘yan tawayen yankin na TPLF da kuma dakarun gwamnati sama da wata daya da ya gabata.

Kayana abinci ya isa ga 'yan gudun hijira
Kayana abinci ya isa ga 'yan gudun hijira UPDEGRAFF / US NAVY / AFP
Talla

Kungiyar agajin ta kasa da kasa Red Cross ta ce manyan motoci bakwai ne dauke da abinci da magunguna da sauran kayayyakin bukata suka isa Makele babban birnin yankin na Tigray mai yawan mutane akalla dubu 500 a yau asabar.

A baya bayan nan ne dai majalisar dinkin duniya ta koka kan yadda rikicin yankin na Tigray ke kara kazancewa bayan da dubban fararen hula suka tsere zuwa kasar Sudan da suka yi iyaka da ita, yayin da kuma a gefe guda kimanin ‘yan gudun hijira dubu 100 daga kasar Eritrea da zaune a yankin na Tigray suka tagayyara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.