Habasha ta ceto Sojinta 1000 da mayakan Tigray suka yi garkuwa da su
Gwamnatin Habasha ta sanar da kubutar da Sojinta dubu 1 da mayakan yankin Tigray suka yi garkuwa da su, sakamakon tashin hankalin da aka samu a yankin.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce cikin wadanda aka kubutar har da mataimakin kwamandan rundunar Sojin da ke kula da Arewacin kasar, wadda mayakan yankin suka kai wa hari a watan jiya.
Gwamnatin kasar ta sanar da murkushe mayakan 'yan tawayen Tigray, yayinda Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi dangane da halin da fararen hula ke ciki a yankin.
Rahotanni sun ce akalla fararen hula sama da dubu 50 suka tserewa rikici domin samun mafaka a makwabciyar kasar Sudan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu