Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Mazauna Tigray za su fara karbar tallafin abinci

Habasaha ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya cikakkiyar damar shigar da kayayyakin agaji cikin yankin arewacin Tigray bayan bangarorin biyu sun cimma mataya a yarjejeniyar da suka kulla.

Wasu mazauna Tigray da ke gudun hijira
Wasu mazauna Tigray da ke gudun hijira AP Photo/Marwan Ali
Talla

Yarjejeniyar wadda Ministan Zaman Lafiya na Habasha ya sanya wa hannu ta amince a shigar da kayayyakin agaji ba tare da shamaki ba ga mutane masu rauni da ke zaune a yankin Tigray da kuma yankunan da ke kan iyakokin Amhara da Afar.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a bara, ya sanar da kaddamar da farmakin ramuwar gayya kan shugabannin jam’iyyar TPLF mai mulkin yankin na Tigray bayan ya zarge su da hannu a harin da aka kai wa sojojin gwamnatin kasar a sansanoninsu.

Dubban mutane sun rasa rayukansu a sanadiyar rikicin da ya barke a yankin, yayin da dubun-dubata suka kaurace wa muhallansu tare da neman mafaka a makwabciyar kasar wato Sudan.

Gwamnatin Habasha dai ta datse hanyoyin sadarwar wayar salula da intenet, sannan ta takaita shiga yankin na Tigray, abin da ya sa aka gaza daukar cikakken rahoton abin da ke wakana a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe makwanni tana gargadin yiwuwar tsundumar al’umma cikin bala’o’i a yankin.

Kimanin mutane dubu 600 mazauna Tigray na rayuwa ne karkashin tallafin abinci kafin barkewar rikicin baya-bayan nan, kuma dubu 98 daga cikinsu ‘yan gudun hijirar Eritrea ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.