Isa ga babban shafi
Habasha

An kashe mutane dubu 50 a Tigray-'Yan adawa

Jam'iyyun Adawar Habasha guda 3 da ke yankin Tigray sun ce, adadin fararen hular da suka mutu sakamakon tashin hankalin da aka samu ya zarce dubu 50 a yankin.

Tun cikin watan Nuwamban bara rikici ya barke a yankin Tigray na Habasha
Tun cikin watan Nuwamban bara rikici ya barke a yankin Tigray na Habasha REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Sanarwar hadin-gwuiwar da Jam’iyyun suka bayar ta bayyana cewar sojojin kasar sun lalata kauyuka da cibiyoyin kula da lafiya da makarantu da wuraren ibada, yayin da aka sace dukiyoyin dake cikinsu.

Jam’iyyun sun ce, akalla mutane sama da miliyan 3 sun tsere daga gidajensu, yayin da har yanzu ake ci gaba da samun kisan gilla da kuma fyade a kowacce rana.

Sao dai kawo yanzu gwamnatin Habasha ba ta mayar da martani ba, sannan ba ta bayar da alkaluman mutanen da suka mutu a sanadiyar rikicin Tigray ba wanda ya barke a cikin watan Nuwamban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.