MDD na fargaba kan yaduwar annobar coronavirus a yankin Tigray
Majalisar dinkin duniya ta bayyana fargaba kan yiwuwar fuskantar yaduwar annobar coronavirus a yankin Tigray mai fama da rikici a kasar Habasha.
Wallafawa ranar:
Gargadin na kunshe cikin wani rahoto da majalisar ta wallafa a karshen makon nan kan fadan da ake gabzawa tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawayen TPLF a yankin na Tigray, wanda ya dubban mutane da muhallansu, gami da rushewar asibitoci da sauran cibiyoyin kula da lafiya.
Sai dai tsawon akalla watanni 2 bayan barkewar rikicin, jami’an agaji sun samu damar fara ayyukan jin kai a yankin.
Rikicin yankin na Tigray dai yayi barazanar zama babban kalubale ga Habsha kasa ta biyu mafi yawan jama’a a Afrika, zalika tuni rikicin ya soma shafar makwabtan kasar da suka hada da Sudan, da kuma Eritrea.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu