Isa ga babban shafi

Rikicin Habasha: Mutane dubu 40 sun tsere Sudan daga yankin Tigray

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane sama da dubu 40 suka tsere daga Habasha zuwa Sudan domin kauce wa tashin hankalin da ake samu a yankin Tigray.

Wasu 'yan gudun hijira.
Wasu 'yan gudun hijira. REUTERS/Esam Omran Al-Fetori
Talla

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce jami’an ta da na Sudan sun yiwa mutane 40,227 rajista daga cikin bakin da suka tsallaka iyaka da Habasha zuwa Sudan domin samun mafaka.

Sanarwar Hukumar ta ce bakin na isa Sudan ne cikin mummunan yanayi sakamakon doguwar tafiyar da suke yi da kafa, ba tare da daukar dukiyoyin da suka mallaka ba.

Sanarwar hukumar na zuwa ne kwana guda bayan da Firaminista Abiy Ahmed ya bai wa shugabannin yankin Tigray wa’adin sa’oi 72 da su mika kan su domin kauce wa afka musu da yaki gadan-gadan.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 45 na mutanen da suka samu mafaka a Sudan yara ne kanana, kashi 4 kuma tsofaffi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.