Mutane dubu 7 sun bar yankin Tigray na Habasaha zuwa Sudan-MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane kusan dubu 7 suka tserewa gidajen su zuwa kasar Sudan domin kaucewa yakin da aka fafata tsakanin sojojin gwamnatin Habasha da 'yan Tawayen yankin Tigray.
Wallafawa ranar:
Hukumar agajin gaggawa ta Majalisar ta ce matsalar ta biyo bayan rikicin da aka samu tsakanin bangarorin biyu wanda ya gamu da suka daga sassan duniya.
Kakakin hukumar Babar Baloch ya ce matsalar yankin ya yi kamari a cikin watanni 3 da suka gabata.
Ko a baya-bayan nan sai da Majalisar ta yi gargadi kan yadda yunwa ke barazana ga yankin na Tigray da har yanzu ke fama da burbushin rikici da kuma mamayar Sojin Habasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu