Yunwa na barazanar halaka dubban mutane a yankin Tigray - MDD
Majalisar dinkin duniya ta bayyana damuwa kan yadda yunwa ke karuwa a yankin Tigray mai fama da rikici a kasar Habasha.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Cikin sabon rahoton da ta wallafa, majalisar dinkin duniyar ta bayyana fadan da ake cigaba da gwabzawa tsakanin dakarun Habasha da ‘yan tawayen TPLF, da matsalar Diflomasiya da kuma katsalandan din wasu kasashen ketare, a matsayin batutuwan dake kara tagayyara al’ummar yankin na Tigray da rikici ya daidaita.
Rahoton ya kara da cewa, kwanaki sama da 100 bayan barkewar yaki a yankin Tigray, har yanzu jami’an agaji sun kasa isa ga mazauna yankunan karkara masu yawan gaske.
A farkon watan Fabarairu kungiyar bada agaji ta kasa da kasa Red Cross tayi gargadin cewa yunwa za ta halaka dubban mutane a yankin an Tigray, muddin aka cigaba da hana jami’an agaji gudanar da ayyukansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu