Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya - Hakkin dan Adam

Yunwa na gaf da tagayyara mutane fiye da miliyan 40 a kasashe 43 - WFP

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta yi gargadin cewar za a iya fuskantar bala’in yunwa mai girman gaske a wasu gwamman kasashe, muddin aka gaza daukar matakan warware matsalar karancin abincin da ake fuskanta yanzu haka.

Wasu yara a Sudan ta Kudu yayin cin abinci a kauyen Nyal.
Wasu yara a Sudan ta Kudu yayin cin abinci a kauyen Nyal. © WFP/Gabriela Vivacqua
Talla

Yanzu haka dai hukumar ta WFP na neman agajin dala biliyan 6 domin tallafawa mutane miliyan 41 da ta ce suna gaf da fadawa cikin bala’in yunwa a kasashe 43, musamman a Sudan ta Kudu, Yemen,  da Habasha wadanda ta ce su ke kan gaba wajen fuskantar matsalar, a yayin da ta bayyana damuwa kan halin da ake ciki a sassan Najeriya da Madagascar.

Yayin jawabi a taron da kasashen kungiyar G20 suka shirya kan ayyukan agaji a garin Brindsisi dake Italiya, shugaban hukumar samar da abincin ta duniya David Beasley ya bukaci kasashe masu arziki da su tashi tsaye wajen kara yawan kudaden tallafin da suke warewa domin agazawa kasashe matalauta da tasirin annobar Korona ya tagayyara, baya ga matsalar yunwar da suke fama da ita a sassansu.

A baya bayan nan kungiyoyin agaji suka bayyana tashe-tashen hankula, tabarbarewar tattalin arziki saboda tasirin annobar Korona, da kuma sauyin yanayi. a matsayin manyan dalilan da suka kara girman matsalar karancin abinci a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.