'Yan tawayen TPLF sun kama sojojin Habasha dubu 7
Mayakan ‘yan tawayen TPLF sun fitar da wani faifan bidiyo dake nuna sojojin kasar Habasha akalla dubu 7 da suka kame yayin yakin da suka gwabza tsawon watanni 8 a yankin Tigray.
Wallafawa ranar:
Bidiyon da jaridar New York Times ta wallafa ya nuna dubban dakarun na Habasha ne a yayin da ake iza keyarsu zuwa wata babbar cibiyar gyaran dabi’u dake Makele babban birnin yankin na Tigray.
A makon da ya kare mayakan ‘yan tawayen TPLF suka yi bazata wajen sake kwace iko da Makele babban birnin yankin, bayan shafe watanni 8 suna gwabza fada sojojin Habasha dake kokarin murkushe su.
Rikicin na Tigray dai na cigaba da daukar hankalin duniya inda a baya bayan nan gwamnatin Habasha ta yi watsi da zargin da ake mata na cewa tana shirin haramtawa kungiyoyin agaji shiga yankin domin tallafawa wadanda yaki ya tagayyara.
Wani rahoton hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya WFP, ya ce mutane akalla miliyan 5 da dubu 200 dake zaman kashi 91 cikin 100 na al’ummar yankin Tigray na cikin bukatar agajin gaggawa na kayayyakin abinci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu