Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

'Yan tawayen Tigray sun kaddamar da sabon farmaki kan dakarun Habasha

‘Yan tawayen dake neman ballewar yankin Tigray sun kaddamar da sabon farmaki kan dakarun gwamnatin Habasha.

Wasu mayakan 'yan tawayen Tigray na TDF yayin kokarin shiga cikin birnin Makele.
Wasu mayakan 'yan tawayen Tigray na TDF yayin kokarin shiga cikin birnin Makele. AFP - YASUYOSHI CHIBA
Talla

Mai magana da yawun ‘yan tawayen Getachew Reda, ya ce sun kaddamar da sabon farmakin ne a ranar Litinin tare da kwace garuruwa da dama ciki har da Korem da kuma Alamata a cewarsa.

Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai rundunar sojin Habasha ba ta ce komai kan ikirarin ‘yan tawayen na Tigray ba, zalika babu tabbas kan gaskiyar bayanan da Reda ya sanar.

Kaddamar da sabon farmakin da ‘yan tawayen na Tigray suka yi ya zo ne makwanni 2 bayan sanar da tsagaita wuta da gwamnatin Habasha ta yi a yankin, sakamakon samun nasarar kwace karin yankunan da ‘yan tawayen ke yi.

Wasu daga cikin dubban sojojin kasar Habasha da 'yan tawayen yankin Tigray suka kama.
Wasu daga cikin dubban sojojin kasar Habasha da 'yan tawayen yankin Tigray suka kama. © Finbarr O'Reilly / The New York Times

A farkon watan nan na Yuli mayakan ‘yan tawayen Tigray suka fitar da wani bidiyo dake nuna sojojin kasar Habasha akalla dubu 7 da suka kame yayin yakin da suka gwabza tsawon watanni 8 a yankin.

Bidiyon ya nuna dubban dakarun na Habasha ne a yayin da ake iza keyarsu zuwa babban gidan Yarin dake Makele babban birnin yankin na Tigray, kwanaki kalilan bayan da ‘yan tawayen suka yi bazata wajen sake kwace iko da birnin na Makele.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.