Isa ga babban shafi
Habasha-Tigray

Habasha ta musanta zargin kawo tarnaki kan agaza wa yankin Tigray

Gwamnatin Habasha ta musanta ikirarin da shugabar hukumar agaji ta Amurka Samantha Power ta yi na cewa tana dakile agajin da ake kai wa yankin Tigray da yaki ya daidaita.

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed.
Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed. © Tiksa Negeri / REUTERS
Talla

A wata sanarwa Power ta ce agajin da ake kaiwa yankin, inda dubun dubatan al’umma ke fuskanta karancin abinci bai wadatar ba, tana mai kashedin cewa akwai hatsarin yankewar abinci.

Hasali ma ta ce ba rashin abinci ne ya janyo karancin abincin ba, amma dakile jami’an agaji da gwamnatin Habasha ke yi ne sila.

Tun a watan Nuwamban bara Tigray ke fama da yaki, tun bayan da Firaminista Abiy Ahmed ya aike da dakaru don takawa wa ‘yan tawayen yankin birki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.