Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

An kame daruruwan 'yan Habasha bisa zarginsu da goyon bayan mayakan Tigray

Jami’an tsaron Habasha sun kame daruruwan mutane tare da rufe wuraren kasuwanci a babban birnin kasar Addis Ababa, bisa zarginsu da tallafawa ‘yan tawayen yankin Tigray dake arewacin kasar ta Habasha da yaki ya tagayyara.

Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. REUTERS - Tiksa Negeri
Talla

Kwamishinan ‘yan sandan birnin Addis Ababa, Getu Argaw, ya ce ana zargin wadanda ake tsare da su da alaka da kungiyar‘ ‘yan tawayen TDF na jam’iyyar TPLF da ke da karfin iko a yankin tun bayan da gwamnatin Habasha ta haramta ta tare da bayyana ta a matsayin ta ‘yan ta’adda.

Bayanai sun ce mutane 323 aka kame da ake zargi da taimakawa mayakan Tigray.

Majiyoyin tsaron Habasha sun ce ana kuma zargin wasu daga cikin kamammun da mallakar makamai, shan sigari, caca, da cin mutuncin tutar kasa da kundin tsarin mulki.

Kamen na zuwa ne yayin da yakin da ake gwabzawa a yankin Tigray ya dauki sabon salo, bayan tura karin sojoji daga yankuna da dama a yakin da ake yi da 'yan tawayen TDF, abinda ya nuna yiwuwar fadadar rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.