Abiy Ahmad ya bukaci 'yan Habasha majiya karfi da su gaggauta shiga aikin soji
Firaministan Habasha Abiy Ahmad ya bukaci al’ummar kasar majiya karfi da su gaggauta shiga aikin soji saboda kazancewar yakin dake gudana a yankunan kasar guda biyu sakamakon daukar makaman da Yan tawaye suka yi suna yakar gwamnati.
Wallafawa ranar:
Yanzu ne lokacin da ya kamata daukaci wani balagage Dan Habasha "ya shiga aikin soji da kuma sojin sa kai domin tabbatar da kishin kasa a cewar pm kasar ta Habasha Abiy Ahmed, watanni 2 bayan da ya ayyana tsagaita buda wuta.
Tun karshen watan yunin wannan shekara rikicin yankin Tigre ya sake fadawa cikin wani mummunan matsayi da ya kai ga tabarbarewar lamuran jinkai a yankin.
An fara gwabza fada ne a watan novemba shekarar da ta gabata bayan da pm Abiy Ahmed ya aika da sojoji a yankin na Tigre domin kawar da gwamnatin yankin, karkashin kungiyar awaren yankin Tigré (TPLF).
A cewar pm da ya taba lashe lambar zaman lafiya ta Nobel a 2019, hare haren an kaddamar da su ne a matsayin ramuwar gayya kan harin da yan awaren yankin na tigre TPLF suka kai kan sansanonin dakarun sojin tarayyar kasar.
A karshen watan Nobembar ne kuma Abiy Ahmed ya shelanta samun nasara a fadan bayan da sojin gwamnatin kasar suka sake kwace Mekele babban birnin yankin.
To sai dai a ranar 28 ga watan juin, mayakan kungiyar yan tawayen -TPLF sun sake kwace birnin na Mekele, tare da kwace mafi yawan yankin na du Tigré a wan safeken.
Bayan tsagaita buda wutar da pm Abiy Ahmed ya kaddamar saboda dalilan jinkai -da kuma janyewar dakarun na habasha daga yankin, dakarun yan tawayen na tigre na ci gaba da kai hare hare a kan yankunan yankuna 2 dake makwaftaka da juna na 'Amhara, dake kudanci da 'Afar, dake gabashin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu