Isa ga babban shafi

Habasha ta koma aikin madatsar ruwa duk da rikicinta da Masar da Sudan

Kasar Habasha ta fara cika madatsar ruwan da ta ke ginawa a karo na biyu matakin da ke tayar da jijiyoyin wuya tsakanin ta da kasashen Masar da Sudan wadanda suka bukaci gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya akai.

Aikin ginin madatsar ruwan Habasha da ya haddasa cece kuce tsakaninta da makwabtanta Masar da Sudan.
Aikin ginin madatsar ruwan Habasha da ya haddasa cece kuce tsakaninta da makwabtanta Masar da Sudan. AFP/File
Talla

Ma’aikatar noman rani a Masar ta bayyana rashin amincewa da matakin, yayin da ita Sudan ta ce bata goyan bayan yin gaban kai da Habasha ke yi.

Kasar Tunisia ta bukaci gudanar da taron kwamitin sulhu akan lamarin domin rage tankiyar da ake samu.

Galibin manyan kasashen Duniya da Amurka akan gaba baya ga kungiyar Tarayyar Afrika sun bukaci daidaitawa da juna tsakanin kasashen 3 makwabtan juna dangane da ginin madatsar ruwan

Sai dai har kawo yanzu an gaza cimma jituwa duk da jerin tattaunawar da bangarorin 3 ke yi baya ga shiga tsakanin da wasu kasashe suka yi ciki har da tarayyar Afrika.

Kasashen Masar da Sudan na ganin aikin ginin madatsar ruwan na Habasha zai katse yawan ruwan da su ke samu baya ga kassara tattalin arzikinsu, a bangare guda Habasha ta sanya buri a ginin wanda ta ce da shi ne za ta dogaro wajen habaka tattalin arzikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.