Isa ga babban shafi
Sudan-Masar-Habasha

Sudan da Masar na tattaunawa da Habasha kan shirinta na ginin madatsar ruwa

Kasashen Sudan Masar da Habasha sun amince da komawa teburin tattaunawa cikin watan nan dangane da takaddamar da ke tsakaninsu kan shirin ginin madatsar ruwan da Habasha ke yi.

Masar da Sudan na caccakar shirin madatsar ruwan na Habasha saboda yadda zai shafi tattalin arzikinsu.
Masar da Sudan na caccakar shirin madatsar ruwan na Habasha saboda yadda zai shafi tattalin arzikinsu. Reuters
Talla

Sau 3 kenan kasashen na zaman tattaunawa amma ba tare da iya cimma jituwa kan takaddamar ba, wadda ta samo asali daga shirin ginin madatsar ruwan Habasha da za ta kasance madatsar ruwa mafi girma da ta faro gininta tun cikin shekarar 2011, amma kuma Sudan da Masar ke ganin zai shafi walwala da tattalin arzikinsu.

Madatsar ruwan mai fadin mita 145, Habasha na kallonta a matsayin sabuwar hanyar habakar tattalin arzikinta, wadda ta zuba makudan kudi wajen gininta, ko da ya ke kammaluwar aikin zai shafi yanayin shigar ruwan tekun nilu cikin kasashen Sudan da Masar.

Ma’aikatar albarkatun ruwa ta Sudan ta sanar da cewa bangarorin 3 sun yi wata ganawa ta bidiyo a jiya Lahadi har ma da wasu jami’an Afrika ta kudu da ke shiga tsakani kan rikicin da ma wakilcin kasasahen Turai.

Sanarwar da ma’aikatar ta Sudan ta fitar ta ce kasashen 3 basu kai ga cimma jituwa ba amma za su ci gaba da kebantacciyar tattaunawa a tsakaninsu, gabanin tattaunawar jumulla a ranar 10 ga watan da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.