Isa ga babban shafi
Amurka

Trump yace Masar zata fasa madatsar ruwan da Habasha ke ginawa

Shugaban Amurka Donald Trump yace babu tantama kasar Masar zata fasa madatsar ruwan da kasar Habasha ke ginawa wanda kasashen Sudan da Habasha da Masar ke takaddama akai saboda yadda zai hana kasar samun ruwan da take bukata.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump MANDEL NGAN / AFP
Talla

Yayin ganawa da manema labarai a fadar sa inda ya bayyana kulla yarjejeniyar huldar diflomasiya tsakanin Sudan da Israila, Trump yace ya fadawa dunkiya da karfi, kuma ya sake nanatawa Masar zata fasa madatsar saboda yadda zata hana kasar samun ruwan da ta saba yi.

Trump yace gina madatsar abin tada hankali ne ganin yadda Masar ta dogara da kogin Nilu dake samar mata da kasha 97 na ruwan da take bukata wajen noma da kuma samun ruwan sha.

Shugaban na Amurka yace kuskure ne Habasha tayi wajen yin gaban kan ta na cigaba da aikin gina madatsar ba tare da sasantawa da makotan ta ba.

Yayin mayar da martani, Firaminista Abiy Ahmed yace kasar sa ba zata bada kai bori ya hau ba dangane da tirsasawa daga kowacce kasa bayan kalaman na shugaba Donald Trump.

Ahmed yace babu wata barazana da zata sanya Habasha sauya matsayin ta dangane da aikin gina madatsar wadda ta fara cika shi da ruwa, kuma kasar ba zata bada kai bori ya hau ba.

Firaministan yace duniya ta shaida cewar, babu wata kasa da ta zauna lafiya bayan takalar Habasha, kuma kan al’ummar kasar a hade yake kuma zasu samu nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.