Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Habasha ta yi barazanar amfani da dukkan karfinta kan 'yan tawayen Tigray

Gwamnatin Habasha ta yi gargadin amfani da dukkan karfinta na soji a Tigray, biyon bayan yadda mayakan ‘yan tawayen yankin na TDF suka fara yunkurin mamaye wasu yankuna da ke makotaka da su.

Dakarun Habasha a garin Humera, yayin sintirin tsare yankin Amhara a ranar 1 ga watan Yulin 2021.
Dakarun Habasha a garin Humera, yayin sintirin tsare yankin Amhara a ranar 1 ga watan Yulin 2021. © REUTERS/Stringer
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Habasha ta ce ‘yan tawayen na Tigray na matsawa gwamnati lambar da za ta tilasta mata amfani da dukkan karfin tsaronta akansu idan suka ki bada hadin kai ga ayyukan jin kai da take yi don kawo karshen rikicin na Tigray cikin lumana.

Da safiyar Juma'ar da ta gabata, kungiyar 'yan tawayen na Tigray tayi watsi da kiraye-kirayen janyewa daga yankuna makwafta na Afar da Amhara da suka mamaye.

Sanarwar ‘yan tawayen ta zo ne kwana guda bayan kwace Lalibela, cibiyar tarihi ta UNESCO da ke yankin Amhara da suka yi, wanda shi ne na baya-bayan nan a rikicin da aka shafe watanni tara ana yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.