Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Ayyukan bada agaji a Tigray na shirin rushewa - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ayyukan bada agajin gaggawa a Tigray da ke arewacin Habasha na shirin tabarbarewa sosai, watanni goma bayan barkewar yaki a yankin tsakanin dakarun kasar ta Habasha da ‘yan tawayen TPLF.

'Yan Habasha daga kabilar Qemant da suka tsere zuwa makwabciyar su Sudan bayan yakin da ya barke a yankin Tigray.
'Yan Habasha daga kabilar Qemant da suka tsere zuwa makwabciyar su Sudan bayan yakin da ya barke a yankin Tigray. ASHRAF SHAZLY AFP
Talla

Grant Leaity, mukaddashin mai kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Habasha ya ce rumbunan tallafin kayayyakin abinci sun kare tun a ranar 20 ga Agusta, a daidai lokacin da yankin na Tigray ya kasance a karkashin katangar da ta datse isar ayyukan jinkai ga dubban mutanen da suke cikin bukatar tallafin gaggawa.

Leaity ya kuma koka kan yadda babu manyan motocin kayayyakin agaji da suka sami damar shiga Tigray tun ranar 22 ga watan Agusta.

Wani matashi yayin aikin rabon abincin da gwamnatin Amhara ta shirya a kusa da kauyen Baker a yankin Tigray na Habasha.
Wani matashi yayin aikin rabon abincin da gwamnatin Amhara ta shirya a kusa da kauyen Baker a yankin Tigray na Habasha. EDUARDO SOTERAS AFP/File

Fada ya barke a watan Nuwamban shekarar 2020 tsakanin sojojin Habasha da mayakan 'yan tawaye masu biyayya ga jam’iyyar TPLF  wacce ke iko da yankin mai kusan mutane miliyan shida.

Kawo yanzu kididdigar hukumomin kasa da kasa ta nuna cewar, dubban mutane suka mutu, yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka tsere daga gidajensu.

Yakin na Tigray da ya dauki tsawon watanni ana gwabza shi, ya haddasa tagayyarar akalla mutane dubu 400 a yankin, wadanda yanzu ke fuskantar yunwa kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.