Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Matsalar yunwa ka iya kaiwa 2022 a Tigray - MDD

Babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths yayi gargadin cewa bukatar neman agajin abinci a yankin Tigray mai fama da rikici a Habasha zai ci gaba har zuwa shekarar 2022 saboda gibin girbin amfanin gonar da za a fuskanta.

'Yan Habasha da suka tserewa rikicin yankin Tigray, yayin da suka yi layin karbar tallafin abinci a sansanin 'yan gudun hijira na Um-Rakoba da ke jihar Al-Qadarif ta kasar Sudan. Ranar 11 ga Disamban, 2020.
'Yan Habasha da suka tserewa rikicin yankin Tigray, yayin da suka yi layin karbar tallafin abinci a sansanin 'yan gudun hijira na Um-Rakoba da ke jihar Al-Qadarif ta kasar Sudan. Ranar 11 ga Disamban, 2020. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Bayan kammala ziyarar kwanaki shida da yayi a kasar Griffiths, ya kuma koka kan karuwar girman kalubalen da al’ummar yankin na arewacin Habasha ke fuskanta na rashin samun kayayyakin agaji na magunguna da abinci abinda ya jefa dubban mutane cikin bala’in yunwa.

Cikin watan Nuwamban shekarar bara Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya aika da sojoji zuwa Tigray domin murkushe jam’iyya mai mulkin yankin da mayakan da ke mata biyayya, matakin da ya ce ya mayar da martani ne ga hare -haren da TPLF ke kai wa sansanin sojojin kasar.

Duk da cewa Firaministan ya bayyana nasara a karashen watan na Nuwamba, dakarun Habasha sun ci gaba da gwabza fada da mayakan ‘yan tawayen na Tigray kusan watanni 10 a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.