Isa ga babban shafi
Habasha-Tigray

Abiy Ahmad ya bar filin daga bayan nasara kan 'yan tawayen Tigray

Firaministan Habasha Abiy Ahmad ya bayyana komawar sa birnin Addis Ababa daga filin daga bayan gagarumar nasarar da ya ce dakarun kasar sun samu akan 'yan Tawayen Tigray.

Firaministan Habasha Abiy Ahmad.
Firaministan Habasha Abiy Ahmad. © Twitter/Abiy Ahmed
Talla

Gwamnatin Habasha tace sojojin gwamnati sun yi nasarar kwace garuruwa masu muhimmanci daga hannun Yan Tawayen wadanda suka hada da Dessie da Kombolcha, irin sa na farko bayan yakin da aka kwashe watanni 13 ana fafatawa.

Firaminista Abiy Ahmad wanda ya jagoranci sojojin kasar zuwa bakin daga domin tinkarar Yan Tawayen da suka kwace wasu garuruwa akan hanyar su ta zuwa Addis Ababa, yace zai koma ofishin sa domin sun samu nasarar farko.

Ahmad yace yakin bai kare ba tukuna, domin har yanzu akwai wasu yankunan dake hannun Yan Tawayen dake dauke da makamai.

Daga cikin yankunan da sojojin gwamnati suka kwace harda garin Lalibela da hukumar UNESCO ta bayyana shi a matsayin wuraren tarihi saboda mujami’ar da aka gina a karni na 12 dake cikin sa.

Sai dai Yan Tawayen TPLF sun yi watsi da ikrarin gwamnatin na samun nasarar da Firaministan yace sun yi na kwace garuruwan da suka kama.

Tabarbarewar rikicin ya sanya kasashen duniya cikin su harda Amurka da Birtaniya da Faransa umurtar Yan kasashen su da su fice daga kasar.

Yanzu haka kungiyar kasashen Afirka ta AU ta nada tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a matsayin jakada na musamman domin sasanta bangarorin dake rikici a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.