Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

MDD za ta tura tawagar masu binciken laifukan yaki zuwa Habasha

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura tawagar masu bincike zuwa kasar Habasha mai fama da rikici, a daidai lokacin da masu bibiyar lamurra a kasar ke gargadin yiwuwar kazancewar lamurra kowane lokaci daga yanzu.

Wasu kauyawa yayin komawa gidajensu daga cin kasuwa a garin Yechila da ke kudu maso tsakiyar yankin Tigray mai fama da rikici. 10 ga Yuli, 2021.
Wasu kauyawa yayin komawa gidajensu daga cin kasuwa a garin Yechila da ke kudu maso tsakiyar yankin Tigray mai fama da rikici. 10 ga Yuli, 2021. © REUTERS/Giulia Paravicini
Talla

Matakin tura tawagar masu binciken na kasa da kasa, ya biyo bayan wani taron gaggawa da kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya mai wakilai 47 yayi, inda ya kada kuri'ar amincewa da kudurin da karamin rinjaye, domin gudanar da bincike kan laifuka da dama da ake zargin bangarorin dake rikici da juna da aikatawa a kasar Habasha tsawon watanni 13.

Tuni dai kasar Habasha ta yi kakkausan suka kan zaman da kuma kudurin hukumar ta kare hakkin dan adam, inda jakadanta Ambasada Zenebe Kebede ya ce ana amfani da ita ne a matsayin wani makami na matsin lambar na siyasa, da kuma wani sabon salon a mulkin mallaka a zamanance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.