Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Habasha ta tsare dubban 'yan Tigray da aka maida su daga Saudiyya

Wani sabon rahoton kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ya bayyana cewa, ana cin zarafin dubban 'yan kabilar Tigray da aka maida su gida daga Saudiyya ta hanyar tsare su, ko kuma batar da su a Habasha.

Wasu daga cikin dubban 'yan kasar Habasha da aka mayar da su gida daga kasar Saudiya.
Wasu daga cikin dubban 'yan kasar Habasha da aka mayar da su gida daga kasar Saudiya. © MoFA / Ethiopia
Talla

Zarge-zargen da Human Rights Watch ta yi karin bayani akai na zuwa ne dai-dai lokacin ake fama da kazamin rikicin da ya barke tsakanin sojojin gwamnatin Habasha da mayakan ‘yan tawayen yankin Tigray da ya barke a watan Nuwamban shekarar 2020, lamarin da ya ui sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane tare da haifar kalubale babba ga ayyukan jin kai.

Gwamnatin Habasha, wadda cikin watan Nuwamba ta kafa dokar ta-baci ta tsawon watanni shida, ta musanta korar ‘yan kabilar Tigray, tare da cewa mutanen da ake zargi da goyon bayan ‘yan tawayen ne kawai, wadanda a watan da ya gabata suka koma yankin nasu.

Sai dai kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Habasha ta yi kiyasin cewa an kama dubban mutane a samamen da dakarun gwamnati suka kai a baya bayan nan.

A cikin rahotonta, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta ce 'yan kabilar Tigray da aka maida su gida daga Saudiyya, inda dubban daruruwan 'yan kasar Habasha suka yi hijira domin neman aiki tsawon shekaru, an ware su ne a babban birnin kasar, Addis Ababa, da sauran wasu wurare ba tare da son ransu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.