Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Jiragen yakin Habasha sun kashe gwamman mutane a sansanin 'yan gudun hijira

Jami’an ayyukan jin kai tare da shaidun gani da ido a Habasha, sun ce wani hari ta sama da aka kai a yankin Tigray da ke arewacin kasar, ya kashe mutane 56 tare da jikkata wasu 30 ciki har da kananan yara a wani sansanin 'yan gudun hijira.

Wadanda suka tsira daga harin sama da sojojin gwamnatin Habasha suka kai kan sansanin 'yan gudun hijira na. Dedebit a yankin Tigray, a yayin da suke karbar magani a babban asibitin Shire Shul da ke garin Dedebit. 8 ga Janairu, 2022.
Wadanda suka tsira daga harin sama da sojojin gwamnatin Habasha suka kai kan sansanin 'yan gudun hijira na. Dedebit a yankin Tigray, a yayin da suke karbar magani a babban asibitin Shire Shul da ke garin Dedebit. 8 ga Janairu, 2022. REUTERS - STRINGER
Talla

Mai magana da yawun rundunar sojin Habasha Kanar Getnet Adane da kuma kakakin gwamnatin kasar Legesse Tulu ba su ce komai kan wanna rahoto ba, wadanda a baya suka sha musanta kaiwa fararen hula farmaki a yankin na Tigray, inda aka kwashe akalla watanni 14 ana gwabza fada tsakanin sojoji da ‘yan tawayen TPLF.

Sai dai kakakin ‘yan tawayen na TPLF Getachew Reda, ya tabbatar da kai mummunan harin kan sansanin ‘yan gudun hijirar na Dedebit, cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Akalla mutane 146 ne suka mutu yayin da wasu 213 suka jikkata a hare-haren jiragen yaki ta sama a yankin Tigray tun daga ranar 18 ga watan Oktoba, a cewar wata takarda da hukumomin agaji suka fitar tare da mikawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.