Isa ga babban shafi

Habasha: Abiy Ahmed ya yi tir da kisan gillar da aka yi wa 'Yan kabilar Oromia

A yayin da aka soma gudanar da jana’izar wadanda suka rasa rayukansu a mummunar kisan kare dangi da akayi wa al’ummar kabilar Oromia na Kasar Habasha, Firaministan Abiy Ahmad ya musanta zargin da ake wa gwamnatinsa.

Firanministan Habasha Abiy Ahmed a shekarar 2021.
Firanministan Habasha Abiy Ahmed a shekarar 2021. AP - Mulugeta Ayene
Talla

Labarin kazamin kisan kare dangin na zuwa ne kwanaki bayan hukumar kare hakkin dan adam ta Habasha ta zargi jami’an tsaron Kasar da hannu a kashe kashen garin Gambella, biyo bayan zargin da ake musu na marawa mayakan OLA baya, wadanda ko a cikin makon da ya gabata sun kai wa al’ummar yankin kudu maso yammacin Kasar hari.

Kashe mutane

Sanarwar da hukumar ta fitar na cewa gida gida jami’an tsaron suka rika bi suna kashe mutane a Gambella dake kan iyaka da Oromia, toh saidai tuni gwamnatin Kasar ta musanta zarge zargen da ake mata, inda tace bata amince da yin duk wani abu na take hakkin bil adama ba, balle na daukan rayuka.

Tuni dai Firaminista Abiy Ahmad ya bayyana a shafinsa na twita cewa ‘ya’yan kungiyar OLA suka aikata aika aikar ne ba tare da sun samu hadin gwiwa daga kowa ba.

Cikin sanarwar da Hukumomin yankin Oromia suka fitar, sun sha alwashin hukunta duk wanda bincike ya tabbatar da hannunshi a faruwar lamarin

'Yan ta'adda

A safiyar asabar  da ta gabata ne dai fada ya barke tsakanin dakarun dake marawa gwamnati baya da mayakan OLA, kungiyar ‘yan tawayen da gwamnatin Habasha ta yi wa lakabi da kasancewa ‘ yan ta’adda.

Yankunan Amharas da Oromos masu dauke da alumma akalla miliyan 115 dai sun kasance mafi girma daga cikin yankunan dake fadin kasar ta Habasha

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.