Isa ga babban shafi

Masu kare hakkin dan Adam na zargin jami'an tsaron Habasha da kashe fararen hula

Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Habasha, ta ce jami’an tsaro sun kashe wasu fararen hula Gambella, bisa zarginsu da hada baki da ‘yan tawayen da suka kai hari a garin dake yankin kudu maso yammacin kasar a farkon makon nan.

Wasu sojojin kasar Habasha yayin atasaye a yankin Amhara, ranar 14 ga Satumban shekarar 2021.
Wasu sojojin kasar Habasha yayin atasaye a yankin Amhara, ranar 14 ga Satumban shekarar 2021. © Amanuel Sileshi AFP/File
Talla

An dai shafe tsawon sa’o’i ana musayar wuta tsakanin jami’an tsaron Habasha da ‘yan tawayen Oromo na OLA da gwamnati ta ayyana matsayin ‘yan ta’adda, yayin harin da aka kai a Gambella ranar Talatar da ta gabata.

Hukumar kare hakkin dan adam a kasar ta ce, bayan da sojoji suka yi nasarar dakile harin da OLA da wata kungiyar masu dauke da makamai suka kai, ne mazauna yankin na Gambella suka fuskanci cin zarafi daban-daban a hannun rundunar ‘yan sandan yankin, kamar yadda shaidu suka tabbatar, da kuma bayanan bidiyon da ta samu.

Wannan ta sanya masu rajin kare hakkin na bil Adam sun bukaci gudanar da bincike tare da tabbatar da bin diddigin ayyukan da jami'an tsaro suka aikata ba bisa ka'ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.