Habasha ta tsaurara matakan tsaro a kan kayan agaji na yankin Tigray
Kasar Habasha ta bukaci tsaurara matakan tsaro akan kayan agajin da ake kaiwa yankin Tigray saboda zargin da take yiwa kungiyoyin agaji da kai wasu kayayyakin da aka haramta zuwa hannun Yan Tawaye.
Wallafawa ranar:
Talla
Mataimakin Firaministan kasar Demeke Mekonen yace ya zama wajibi jami’an tsaro sun sanya ido sosai domin ganin cewar ba’a baiwa Yan Tawayen TPLF kayayakin da aka haramta ba.
Mekonen yace ya gano cewar ana safarar man fetur fiye da yadda aka amince zuwa yankin tare wasu kayayyakin da aka haramta wadanda Yan tawayen ke amfani da shi wajen kai hari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu