Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Wasu likitoci a Habasha sun shiga barar abinci saboda yunwa

Majalisar Dinkin Duniya tace, kusan kashi 40 cikin 100 na al'ummar yankin Tigray da ke fama da yaki a kasar Habasha na fama da "matsanancin karancin abinci.

'Yan Habasha da suka tserewa rikicin yankin Tigray, yayin da suka yi layin karbar tallafin abinci a sansanin 'yan gudun hijira na Um-Rakoba da ke jihar Al-Qadarif ta kasar Sudan. Ranar 11 ga Disamban, 2020.
'Yan Habasha da suka tserewa rikicin yankin Tigray, yayin da suka yi layin karbar tallafin abinci a sansanin 'yan gudun hijira na Um-Rakoba da ke jihar Al-Qadarif ta kasar Sudan. Ranar 11 ga Disamban, 2020. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Kiyasin abinci na baya-bayan nan da Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta fitar ranar Juma'a (28 ga watan Janairu), ya ce jimillar mutane miliyan 4.6, wato kashi 83% na al'ummar Tigray, ba su da isasshen abinci, yayin da miliyan biyu (kusan kashi 40%). ) kef ama da yunwa.

Wasu rahotannin na cewa lamarin ya tilastawa wasu daga cikin ma'aikatan jinya da kuma likitoci a babban asibiti a yankin Tigrai yin bara domin neman abinci.

Daya daga cikin likitocin ya ce, tsawon watanni takwas ba a biya su albashi ba, lamarin da ya jefa su bin wasu hanyoyin da za su tallafa wa iyalansu.

Rahoton wanda shi ne na farko kan tabbataccen kididdigar samar da abinci cikin watanni shida da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana irin bala'in jin kai a arewacin kasar Habasha, inda dakarun da ke goyon bayan gwamnati da 'yan tawayen kabilar Tigrai (TPLF) ke fafatawa da juna tun daga cikin watan Nuwambar shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.