Mutane 750 ne aka kashe a arewacin Habasha a 2021
Hukumar kare hakkin dan adam ta kasar Habasha a ta ce akala fararen hula 750 ne aka kashe a yankunan Amhara da Afar na Kasara a rubu’i na biyu na shekarar 2021.
Wallafawa ranar:
Rahoton hukumar ya kuma kawo bayanai a kan keta haddin dan adam, cin zarafi, azabtarwa da kuma tabbatar da bacewar mutane.
Hukumar kare hakkin dan adam na Habashar ta ce akalla fararen hula 403 ne suka mutu, 309 kuma suka samu rauni sakamakon samame ta sama, da hare haren jirage marasa matuka da kuma harbi da manyan makaman atilari tun da ‘yan tawayen Tigray da ke yaki da gwamnatin kasar suka kaddamar da hare hare a kan yankunan da ke makwaftaka da su arewacin Habasha a cikin watan Yulin shekarar da ta gabata.
Akalla mutane 346, wadanda fararen hula ne suka mutu a kashe kashen gilla da bangarorin da ke yaki da juna suka aiwatar.
Hukumar ta kuma zargi ‘yan tawayen Tigray da cin zarafi da suka hada da fyade, azabtarwa, sata da kuma barnata kadarorin gwamnati kamar asibitoci da makarantu a yakuna 2 da ke iyaka da yankin Tigray.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu