Isa ga babban shafi
Habasha-Tigray

'Yan tawayen Tigray sun janye daga yankuna arewacin Habasha 2

‘Yan tawayen yankin Tigray na Habasha sun sanar da janyewa daga yankuna biyu na arewacin kasar don komawa gida a wani yunkuri na tsagaita rikicin watanni 13 da suka shafe suna fafatawa da dakarun gwamnati.

Wasu mayakan 'yan tawayen Tigray na Habasha.
Wasu mayakan 'yan tawayen Tigray na Habasha. AFP - YASUYOSHI CHIBA
Talla

Mai Magana yawun ‘yan tawayen Getchew Reda ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa mayakansu sun kammala ficewa daga yankunan Amhara da Afar don bayar da damar isar da kayakin agaji.

Sai dai mai Magana da yawun Firaminsita Abiy Ahmad, Billene Seyoum ta ce sanarwar 'yan tawayen wani yunkuri ne na boye koma bayan da suka samu daga sojojin gwamnati.

Ficewar mayakan ‘yan tawayen dai ya iya samar da damar tattaunawar sulhu tsakaninsu da gwamnatin Habasha da nufin kawo karshen rikicin wanda ya kashe dubunnan fararen hula baya ga tilasta da dama tserewa daga muhallansu.

Rikicin na watanni 13 dai ya jefa Habasha a gagarumar matsalar bukatar dauki baya ga tagayyara mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.