Isa ga babban shafi

Yunwa na kashe mutum guda duk bayan dakika 48 a gabashin Afrika- Rahoto

Kungiyar agaji ta OXFAM tare da abokiyar aikinta ta ‘Save the Children’ sun ce akalla mutum guda ke mutuwa sakamakon yunwa a kasa da dakika 48 kowacce rana a kasashen Habasha da Kenya da kuma Somalia sakamakon yunwa.

Kungiyoyin OXFAM da Save the Children sun ce matukar ba a dauki matakan da suka kamata wajen tunkarar matsalar ba, ko shakka babu illar da yunwa za ta yiwa yankin ka iya kai wani yanayi da baza a magance shi ba.
Kungiyoyin OXFAM da Save the Children sun ce matukar ba a dauki matakan da suka kamata wajen tunkarar matsalar ba, ko shakka babu illar da yunwa za ta yiwa yankin ka iya kai wani yanayi da baza a magance shi ba. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Rahotan kungiyoyin biyu yace bayan sama da shekaru 10 da aka fuskanci matsalar yunwa a wannan yanki wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 260,000 a Somalia, wadanda sama da rabin su kananan yara ne, duniya na fuskantar wani sabon barazana a Yankin na Gabashin Afirka.

Kungiyoyin sun ce mutane sama da rabin miliyan guda ne ke fuskantar tsananin yunwar a wasu yankunan kasashen Somalia da Habasha, yayin da ake da sama da mutum miliyan 3 da rabi a kasar Kenya.

Kungiyoyin sun bayyana cewa, hakan na da nasaba rikice-rikice da sauyin yanayi da kuma tsadar kayan abinci da yankin ke fama da su, suna masu dora alhakin fadawa wannan matsala kan gazawar ‘yan siyasa.

OXFAM da Save the Children sun soki gwamnatocin kasa da kasa da ke jinkiri wajen tinkarar bala’in cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.