Isa ga babban shafi
Yunwa

Mutane miliyan 20 na cikin barazanar yunwa a Afrika

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ya nuna cewa mutane miliyan 20 ne ke fuskantar barazanar yunwa a Afirka yayin da fari ke kara ta'azzara, musamman a kasashen Kenya, Somaliya da kuma Habasha.

Yadda fari ya lalata wata konar masara.
Yadda fari ya lalata wata konar masara. AFP/File
Talla

Farin da aka kwashe watanni ana yi ya bar yankin na Afirka da ke gab da fuskantar bala'in jin kai cikin mummunann yanayi in ji Majalisar Dinkin Duniya, inda ya lalata amfanin gona da dabbobi tare da tilasta wa dimbin jama'a barin gidajensu domin neman abinci da ruwa.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 40 cikin 100 na al’ummar Somaliya fuskantar matsanancin karancin abinci, a Kenya kuwa, mutane rabin miliyan ne ke gab da fuskantar matsalar yunwa.

Adadin karancin abinci mai gina jiki a kudanci da kudu maso gabashin Habasha da fari sun yi kamari, yayin da arewacin kasar ke fama da yakin watanni 17 tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen Tigray.

Hukumar kula da abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa, wasu sassan kuryar gabashin Afirka da ke fama da fari sun riga sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon tashe-tashen hankula, fatara da kuma mamayewar fari.

Hukumar ta yi gargadin cewa rashin isassun kudade na iya haifar da bala'i, inda ta yi kira da a samar da dala miliyan 473 cikin watanni shida masu zuwa.

Kokarin da aka yi a baya a watan Fabrairu ya tara kasa da kashi hudu na kudaden da ake bukata, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Gabashin Afirka ya sha fama da matsanancin fari a shekarar 2017 amma matakin jin kai da aka dauka cikin gaggawa ya dakile matsalar yunwa a Somaliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.