Isa ga babban shafi

An tara kudin agaza wa kasashen Afrika masu fama da yunwa

Wani taron bada agaji da aka gudanar a birnin Geneva, ya tara Dala biliyan 1.39 domin tallafa wa yankin Kahon Afrika mai fama da matsalar fari, lamarin da ke barazanar jefa miliyoyin mutanen yankin cikin yunwa.

Kasashen yankin kahon Afrika na fama da barazanar yunwa
Kasashen yankin kahon Afrika na fama da barazanar yunwa REUTERS/African Union-United Nations
Talla

Kasashen Habasha da Kenya da Somalia za su ci gajiyar gagarumin tallafin kudaden ganin yadda yankinsu ke fama da matsalar fari mafi muni cikin shekaru 40  kamar yadda wata sanarwar Majalisar Dinkin Duniya ta ce.

Matsalar ta fi kamari a wasu yankuna shida na Somalia, inda aka ce, lallai akwai yiwuwar samun yunwa muddin aka rasa wadataccen ruwan sama a kakar bana, sannan kuma farashin kayayyakin abinci ya yi tashin goron zabbi, gami da samun karancin tallafa wa mabukata.

Tun da fari, kungiyoyin agaji sun bukaci a tara Dala biliyan 1.4 domin fitar da yankin na Kahon Afrika daga kangin yunwa.

Yanzu haka, kungiyoyin na gaaji za su yi amfani da kudaden wajen samar da abinci cikin gaggawa da kuma kula da marasa lafiya, baya ga samar da magunguna ga daddobin da ake kiwatawa a yankin kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta fadi.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce, sama da mutane miliyan 6 na fama da matsancin karancin abinci a Somalia, inda a Kenya adadinsu ya kai miliyan 3.5, yayin da a Habasha ake da miliyan 6.5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.