'Yan tawayen Tigray sun yi barazanar watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta
Kwamandan 'yan tawayen yankin Tigray da ke arewacin Habasha ya sha alwashin cewa za su ci gaba da fafatawa da dakarun gwamnati har sai an cika sharuddan da suka gindaya na tsagaita wuta.
Wallafawa ranar:
Janar Tsadkan Gebretensae ya ce burinsu shi ne tilastawa gwamnatin Habasha janye shingen da ta sanya a yankin tare da amincewa da a warware rikicin da ke tsakaninsu a siyasance.
Gwamnati dai ta musanta ikirarin ‘yan tawayen na cewa dakarunta sun yi wa yankin na Tigrai kawanya gami da hana shiga ko fita daga cikinsa, kana kuma ta yi watsi da batun tattaunawar sulhun.
Rayukan dubban mutane ne dai suka salwanta tun bayan barkewar yaki a yankin Tigray cikin watan Nuwamban bara waccan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu