Isa ga babban shafi

Kungiyar CPJ ta bukaci yan tawayen Tigray su sako wasu 'yan jarida 2

Kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta duniya ta bukaci ‘yan tawayen Tigray na Habasha da su gaggauta sakin wasu ‘yan jarida 2 da ta kama, wadanda da ke aiki da wata kafar yada labarai a yankin da yaki ya daidaita a arewacin kasar.

Mayakan kungiyar Tigray a Habasha
Mayakan kungiyar Tigray a Habasha AFP - YASUYOSHI CHIBA
Talla

‘Yan tawayen Tigray, wadanda suke yaki da gwamnatin Habsha yau watanni 20 kenan, sun sake karbe iko da yankin nasu a watan Yunin shekarar 2021, inda suka hambarar da gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa a yankin.

Kungiyar kare hakkin ‘yan jaridar ta ce ‘yan tawayen sun kama wadannan ‘yan jaridanda ke aiki da tashar talabijin Tigray a watan Mayu da Yunin wannan shekarar.

A watan maris ne 'Yan Tawayen yankin Tigray na Habasha suka amince da tayin tsagaita wutar da gwamnati ta gabatar domin bada damar gudanar da ayyukan jinkai a yakin da aka kwashe watanni 17 ana fafatawa a tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.