Isa ga babban shafi
MDD-Habasha

Mahukuntan Habasha sun amince da shigar da kayakin agaji yankin Tigray

Karon farko tun bayan da bangaren gwamnati da ‘yan tawayen Habasha suka sanar da tsagaita wuta, motoci 20 dauke da kayayyakin jinkai sun shiga yankin Tigray da ke arewacin kasar ta Habasha.

Kayakin agaji na Majalisar Dinkin Duniya.
Kayakin agaji na Majalisar Dinkin Duniya. AFP/File
Talla

Wadannan motoci sun shiga yankin ne a dai dai lokacin da alkaluma ke tabbatar da cewa kashi 90% na mutane milyan biyar da rabi da ke rayuwa a yankin na Tigray na cikin yanayi na bukatar taimakon abinci a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Wannan dai na nuni da cewa ana bukatar bai wa akalla manyan motoci dari daya dauke da kayan abinci shiga yankin domin wadatar da al’ummar, kuma tun a watan disambar da ya gabata ne aka kange hanyoyin da ke bayar da damar shiga yankin da ke arewacin kasar Habasha.

Hukumar Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta ce bayan isar wannan ayari da ke kunshe da motoci 20, hukumar da sauran kungiyoyin agaji na kasa da kasa na fatan bangarorin biyu za su ci gaba da mutunta tsagaita wutar don samun damar kai wa jama’a dauki.

Hukumar agajin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ta ce rashin samun damar isar da kayayyakin agaji ga mazauna yankin na Tigray, abu ne zai kara milyoyin rayuka a cikin hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.