Isa ga babban shafi
Habasha-Tigray

'Yan tawayen Tigray sun amince da tsagaita wuta a yakinsu da Sojin Habasha

'Yan Tawayen yankin Tigray na Habasha sun amince da tayin tsagaita wutar da gwamnati ta gabatar domin bada damar gudanar da ayyukan jinkai a yakin da aka kwashe watanni 17 ana fafatawa a tsakanin bangarorin biyu.

A jiya Alhamis ne Firaminista Abiy Ahmed ya mikawa 'yan tawayen bukatar tsagaita wutar yayinda a yau juma'a suka amince a kokarin isar da kayakin agaji yankunan da yakin ya daidaita.
A jiya Alhamis ne Firaminista Abiy Ahmed ya mikawa 'yan tawayen bukatar tsagaita wutar yayinda a yau juma'a suka amince a kokarin isar da kayakin agaji yankunan da yakin ya daidaita. AP
Talla

Sanarwar da 'Yan tawayen suka gabatar ta ce a shirye su ke su aiwatar da shirin tsagaita wutar cikin gaggawa, yayinda suka bukaci gwamnatin kasar da ta hanzarta wajen gabatar da kayan agaji a Yankin Tigray inda dubun dubatan mutane ke fuskantar bala’in yunwa.

Tun barkewar tashin hankalin a watan Nuwambar shekarar 2020, dubban mutane sun rasa rayukan su, yayinda wasu kuma suka tsere daga gidajensu domin tsira da rayukansu, a dai dai lokacin da yakin ya yadu zuwa yankunan Amhara da Afar.

Firaminista Abiy Ahmed ya gabatar da shirin tsagaita wutar jiya alhamis, inda ya bayyana fatar ganin ya taimaka wajen saukakawa jama’a radadin yakin da su ke ji da kuma bada damar raba kayan agaji.

Ahmed ya kuma bukaci 'Yan Tawayen Tigray da su kaucewa kai hari lokacin tsagaita wutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.