Isa ga babban shafi
Habasha -Tigray

Abiy Ahmed ke da babban nauyin kawo karshen zubar da jini a Tigray-Nobel

Kwamitin da ke bayar da kyautar zaman lafiya ta Nobel a Norway, ya ce Firaministan Habasha Abiy Ahmed wanda ya lashe lambar yabon a 2019, na dauke da nauyi na musamman wajen kawo karshen zubar da jini a yankin Tigray.

Wani yanki a Tigray na Habasha da ke fama da rikici.
Wani yanki a Tigray na Habasha da ke fama da rikici. AP
Talla

Sanarwar da kwamitin ya fitar ta ruwaito shugaba Berit Reiss-Anderson na cewa rawar da Abiy Ahmed ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a Habasha bayan hawansa mulki, ya na basu kwarin gwiwar cewa zai iya taimakawa wajen kawo karshen rikicin yankin Tigray a yanzu.

Tun cikin watan Nuwamban 2020 yankin Tigray na Habasha ya fada rikici da ya juye zuwa yaki bayan da gwamnatin kasar ta zargi ‘yan tawayen TPLF da kai wa dakarunta farmaki a sansaninsu da arewaci.

Zuwa yanzu dubunnan fararen hula da jami’an tsaro suka mutu sanadiyyar fada tsakanin dakarun gwamnatin ta Habasha da ‘yan tawayen Tigray baya miliyoyi da rikicin ya tilastawa barin matsugunansu.

Sanarwar ta kwamitin Nobel ta ce halin da ake ciki a yankin Tigray da sauran yankunan da rikicin ya fantsama kama daga karancin abinci da rashin kayakin agaji ba abin karba ba ne, wanda ke bukatar shugaba Abiy Ahmad ya taka rawar gani don tabbatar da ayyukan jinkai da kuma dakile tashe-tashen hankulan.

Sai dai a martanin kakakin Abiy, Billene Seyoum ta ce tuni shugaban na Habasha ya tunkari matsalar ta hanyar daukar matakan da suka dace don sauke nauyin da ke kansa.

Acewar Seyoum tun a bara shugaba Abiy Ahmad ya kawo karshen rikicin ta hanyar shiga cikin dakarun da suka murkushe barazanar ‘yan tawayen na Tigray wadanda Majalisar kasar ta ayyana a ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.