Isa ga babban shafi

Banbancin launin fata ne ya hana Tigray samun agaji daga kasashe- Tedros

Darakta Janar na hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi ikirarin cewa banbancin launin fata ne ya sanya kasashen Duniya kin mayar da hankali don taimakawa kan halin da miliyoyin fararen hula ke ciki a yankin Tigray na Habasha da ya yi fama da yaki.

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. AP - Salvatore Di Nolfi
Talla

A jawabinsa yayin taron masu ruwa da tsaki a harkokin agaji na duniya da ya gudana ta bidiyo, Dr Tedros ya diga ayar tambaya game da yadda kasashen Duniya suka mayar da hankali wajen taimakon Ukraine amma suka kawar da kai ga yankin na Tigray duk da halin da ake ciki.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa duk da yadda fararen hula suka fi wahaltuwa a Tigray amma hankalin duniya ya fi karkata wajen Ukraine saboda kasancewarsu farar fata.

A cewar shugaban na WHO, yanzu haka mutane miliyan 6 a yankin na Tigray basu samun isasshen abubuwan tafiyar da rayuwa da suka kunshi abinci da ruwan sha, haka zalika babu kulawar lafiya babu kuma makarantu saboda yadda yaki ke ci gaba da daidaita yankin.

Tedros wanda ya bayyana rikicin yankin na Tigray da kuma halin fararen hula ke ciki a yankin da mafi munin tashin hankalin da ke bukatar agajin gaggawa, ya ce laifin yankin na Tigray daya shi ne kasancewa na bakar fata, banda haka da ya samu daukin da ya ke bukata.

Ko a cikin watan Aprilun da ya gabata yayin makamancin jawabin da Tedros ya gabatar, ya yi tambayar ko rayukan bakar fata da na farar fata na iya samun daidaito ta fuskar agaji daga manyan kasashen duniya?

Shi ma daraktan kula da ayyukan agaji na WHO Mike Ryan ya bayyana damuwa da rashin kulawar kasashen Duniya game da fargabar fuskantar matsananciyar yunwa da fari a yankin kahon Afrika, wanda ya ce har zuwa yanzu babu alamun akwai masu shirin taimakawa.

Hukumar WHO dai ta bukaci agajin dala miliyan 123 don magance matsalar cutukan da yunwa ta haifar a yankin na kahon Afrika da mutane miliyanb 200 ke rayuwa cikin tagayyara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.