Isa ga babban shafi
MDD-YUNWA

Fari zai jefa mutane miliyan 13 cikin matsananciyar yunwa a kahon Afrika- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yadda mutane miliyan 13 ke fuskantar matsananciyar yunwa a kassahen Kenya da Somalia da kuma Habasha dai dai lokacin da yankin na kahon Afrika ke fuskantar fari karon farko cikin shekaru 10.

Wannan ne karon farko da yankin na kahon Afrika ke fuskantar matsananciyar yunwa tun bayan makamanciyarta a Somalia da ta hallaka mutane dubu 250 a shekarar 2011.
Wannan ne karon farko da yankin na kahon Afrika ke fuskantar matsananciyar yunwa tun bayan makamanciyarta a Somalia da ta hallaka mutane dubu 250 a shekarar 2011. ANIS MILI AFP
Talla

Shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa wannan ne fari mafi muni da yankin na kahon Afrika ke fuskanta tun bayan shekarar 1981 wanda zai shafi mutane miliyan 13 a kasashen 3 da suka kunshi Kenya da Somalia da kuma Habasha.

Rahoton MDD da ke gargadi kan yunwar a kasashen 3, ya alakanta matsalar katsewar damunar da suka fuskanta cikin shekaru 3 a jere.

Acewar Majalisar, katsewar damunar da kasashen 3 suka fuskanta a shekaru ukun baya-bayan nan ya haddasa lalacewar amfanin gona da mutuwar tarin dabbobi baya ga tilastawa iyalan da suka dogara da noma wajen rayuwa yin kaura daga matsugunansu zuwa wasu yankunan kasar.

Shugaban hukumar abincin shiyyar gabashin Afrika Michael Dunford ya bayyana rashin wadatuwar ruwa a kasashen da lalacewar kasar shuki a matsayin babbar barazana kari kan hasashen fuskantar karin karancin ruwan sama a watanni masu zuwa.

Rahoton ya ruwaito Mr Dunford na cewa amfanin gona sun lalace, dabbobi da tsirrai na mutuwa yayinda yunwa ke karuwa a kasashen 3, wanda ke bukatar agajin gaggawa don kaucewa sake fuskantar mace-macen da aka gani a Somalia cikin shekarar 2011 inda yunwa ta kashe mutane dubu 250 sakamakon farin da kasar ta gani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.