Isa ga babban shafi

China ta yi tayin shiga tsakani don sasanta kasashen yankin kahon Afrika

China ta yi tayin shiga tsakani don warware rikicin da ke tsakanin kasashen yankin kahon Afrika dai dai lokacin da suke wani taron tsaro da zaman lafiyar yankin a birnin Addis Ababa na Habasha.

Shugaban kasar Habasha, Abiy Ahmed.
Shugaban kasar Habasha, Abiy Ahmed. AP - Mulugeta Ayene
Talla

Taron wanda na hadin gwiwa ne tsakanin kasar ta Sin da kasashen yankin mai taken tsaro shugabanci da ci gaban yankin kahon Afrika na da nufin lalubo hanyar warware matsalolin tsaro da tankiyar da kasashen ke fuskanta tsakaninsu.

Jakadan China na musamman ga yankin, Xue Bing ya ce kasarsa a shirye ta ke ta shiga tsakanin don samar da zaman lafiya tare da mutunta bukatun kowacce kasa ba tare da Fifita wata akan wata ba.

A cewar Bing wajibi ne a girmama iko da martabar kowacce kasa tare da kange saura daga yiwa kowacce kasa a yankin katsalandan a harkokin cikin gidanta, yana mai cewa kasar sa na da amannar cewa kasashen yankin za su bayar da cikakken hadin kai wajen sulhunta junansu.

Ita kanta Habasha da ke matsayin jagora a yankin na fama da matsalar tsaro bayan yakinta da ‘yan tawayen TPLF a yankin Tigray tun watan Nuwamban 2020 ko da ya ke Firaminista Abiy Ahmed ya bayyana shirin tattaunawar sulhu da su a makon jiya.

Taron kasashen na kahon Afrika da ake shirin kammala shi a yau talata, ya samu halartar wakilcin kasashen Djibouti da Kenya da Somalia da Sudan ta kudu sai kuma Sudan da Uganda baya ga Habasha da ta karbi bakoncin taron kana China mai shiga tsakani yayinda Eritrea ta kauracewa taron.

China na da sansanin Sojinta guda daya tilo a nahiyar Afrika da ta girke a Djibouti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.