Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Tigray sun zargi Sojin Habasha dana Eritrea da kai musu hari

‘Yan tawayen yankin Tigray na Habasha sun yi ikirarin yi musu wani luguden wuta a safiyar yau alhamis a farmakin hadakar da Sojin kasar da taimakon na Eritrea suka kai kan yankin.

Tankar yakin Sojin Habasha.
Tankar yakin Sojin Habasha. © Stringer/File Photo/Reuters
Talla

Sanarwar da ‘yan tawayen suka fitar ta ce yanzu haka Habasha ta girke tarin dakaru a Eritrea wanda za ta rika amfani da su wajen kai hare-haren hadin gwiwa kan yankin na Tigray.

Sanarwar dauke da sa hannun kwamandan ‘yan tawayen na Tigray, ta ce Sojin Habasha sun fara atisayen hadakar ne da Sojin Eritrea don kammala murkushe yankin wanda ke halin matsanancin talauci da bukatar agaji.

Sai dai kamfanin dillancin labaran Faransa AFP bai kai ga tabbatar da wannan ikirari na ‘yan tawayen ba, game da atisayen hadakar da dakarun kasashen biyu suka fara don murkushe ‘yan tawayen, la’akari da yadda ake da matsalar sadarwa a arewacin kasar ta Habasha.

Wata tattaunawa da AFP ta yi da kakakin ‘yan tawayen Kindeya Gebhrehiwot y ace dukkanin hare-haren Sojin na fitowa ne daga Eritrea musamman na Sojin sama.

Gwamnatin Habasha dai ba ta ce uffan game da zargin ‘yan tawayen ba, kan hare-haren hadin gwiwar a yankin Tigray ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.